Adadin basussukan da Najeriya ta ciwo da suka hada da na gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohin kasar 36, da kuma babban birnin kasar yanzu sun kai naira triliyan 31 da biliyan 9, kwatankwacin dala biliyan 85 da miliyan 897 a cewar alkaluman kididdiga daga ofishin kula da basussukan Najeriya wato DMO, lamarin da wasu ‘yan kasar ke alakantawa da karin da aka samu a farashin man fetur da wutar lantarki saboda sharudan da babban bankin duniya, da bankin bada lamuni na IMF suka bayar.
Honarabul Abubakar Yunusa Ahmad, mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba a jihar Gombe, ya ce yanayin da Najeriya da kuma kasashen duniya baki daya suka samu kansu a ciki ne ya sa aka shiga wannan yanayin. Ya kuma ce karin da aka samu ba zai rasa nasaba da basussukan da daidaikun gwamnonin kasar suka ciwo ba.
Shi ma masanin harkokin tattalin arziki, Kasim Garba Kurfi ya yi tsokaci a kan wannan lamari inda ya ce, idan Najeriya zata zauna ta dubi abinda ya kamata a yi to tabbas yanayin zai wuce.
Alkaluman kididdigar da aka fidda a watan Maris sun yi nuni da cewa an ciwo bashin naira triliyan 28 da biliyan 628 kwatankwacin dala biliyan 79 da miliyan 303.
Alkaluman da ofishin DMO ya fidda sun bayyana cewa an samu kari a basussukan da naira triliyan 2 da biliyan 381 saboda rancen da aka karbo don cike gibin da aka samu a kasafin kudin shekarar 2020 da aka yi wa garambawul na dala biliyan 3 da miliyan 360, an karbo rancen ne daga bankin bada lamuni na IMF, da sabbin basussukan cikin gida da suka hada da bashin Sukuk na naira biliyan 162 da milyan 557, da takardar yarjejeniyar promissory note, da kuma hakokkin masu fitar da kaya zuwa wajen kasar.
Ofishin na DMO na sa ran cewa yawan basussukan da ke kan gwamnatin Najeriya zai karu idan aka yi la’akari da karin da aka samu a basussukan cikin gida da kuma kudadden da zasu shigo daga babban bankin duniya, da bankin bada lamuni na IMF, da bankin bunkasa addinin musulunci da kuma bankin raya kasashen nahiyar Afrika wanda aka karbo domin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2020.
Sauri cikakken rahoton Halima Abdulra’uf.
Your browser doesn’t support HTML5