Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitocin Dabbobi Sun Ceci Ran Kunkuru Mai Shekaru 75


Wani Jami'in kula da gandun daji a kasar Kenya yana rike da kunkuru.
Wani Jami'in kula da gandun daji a kasar Kenya yana rike da kunkuru.

Likitocin dabbobi a jihar Sokoto sun ceci ran wani tsohon kunkuru, da ya zama sananne a garin Argungu ga ke jihar Kebbi.

Tawagar likitocin da ta kunshi likitocin asibitin dabbobi dake cikin garin Sokoto, da na sashen koyon aikin jinyar dabbobi na makarantar aikin jinya ta jami’ar Usmanu Danfodiyo, sun sami nasarar ceto ran kunkurun mai shekaru saba’in da biyar a duniya ne, bayan da suka yi mashi tiyata a gadon baya sakamakon mummunan rauni da ya ji.

Lamarin ya faru ne ranar Talata a garin Argungun kafin aka dauki kunkurun zuwa garin Sokoto, inda aka hada kan kwararrun likitoci da suka yi mashi jinya.

Bayanin da ya fito daga asibitin dabbobin na Sokoto ya ce, Kunkurun da aka kai asibitin daga karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi, ya sami mummunan rauni ne bayan da wata babbar mota kirar Hilux ta bi ta kansa, ta fasa masa gadon baya.

Kunkuru mafi sauri
Kunkuru mafi sauri

Rahotanni dai na nuni da cewa, likitocin da suka yi wa kunkurun tiyata, sun yi amfani da wata irin waya da ke rike kashi, suka hada inda ya sami karaya kafin maida shi Argungu, bayanda suka gamsu da yanayin da ya ke ciki.

Bincike na nu ni da cewa, mazauna garin Sokoto dake bin titin Barth, sun saba ganin wani tsohon kunkuru irin wannan, wanda ya kan rika fitowa daga gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Dr. Garba Nadama, yana yawo a gaban gida.

Wannan kunkurun da aka yi wa aiki, ba shi ne kunkuru mafi tsufa da aka saba gani a Najeriya ba.

A farkon watan Oktoba shekarar da ta gabata ne aka sanar da mutuwar Kunkurun da aka hakikanta cewa, ta fi kowanne kunkuru tsufa a nahiyar Afrika.

Wani katon kunkuru a wurin shakatawa na La Vanille Nature Park, Mauritius
Wani katon kunkuru a wurin shakatawa na La Vanille Nature Park, Mauritius

Kunkurun da ake kira Alabgba (dattijo), ta rasu ne a fadar Sarkin Ogbomoso Oba Jimoh Oyewumi tana da shekaru 344 a duniya.

An nunawa kunkuru Alagba gata ainun a fadar Sarkin, inda aka dauki ma'aikata biyu domin kulawa da ita, kama daga bata abinci da kuma kulawa da dukan bukatunta na yau da kullum, har lokacin da ta rasu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG