Barkewar Sabuwar Matsalar Mai a Arewacin Najeriya

Wata ma'aikaciyar wani gidan mai

Al’amarin dai ya fara sukurkuta harkokin sifiri da zirga zirgan jama’a

Yau dai an shiga rana ta uku kennan da barkewar sabuwar matsalar mai a birni da kewayen Kano.

Rahotani daga jahohin Jigawa da Katsina da wasu bangarori na arewacin Najeriya, na nuni da yadda karancin man ya sake kuno kai bayan wadatuwa da albarkatun man fiye da watani uku a baya.

Al’amarin dai ya fara sukurkuta harkokin sifiri da zirga zirgan jama’a, a yankuna wadannan jihohi, masamma ma acikin biranai, sai dai shugaban siyar Kano, na kungiyar dillalan mai ta Najeriya, Alhaji Bashir Dan Malam, ya bayyana dalilan da suka haifar da matsalar a wannan karon.

Ya ce “na farko dai mun tsinci kan mu wurin da muke siyan wanna kayan sun kara mana farashi na Gwamnati akwai wurin da ake siyar mana da shi akan Naira 85, 86.5 akwai 84.5, a Lagos, Calabar, Warri da Port Harcourt.

Na biyu akwai hanya da ta lalace Direba sai ya kwana biyar shida shima ya taimaka abisa wanna, sannan kayan ma akwai karanci shi a wuraren da muke siyan shi.