Wasu malaman makarantun sakandare na jihar ta Neja sun koka tare da nuna damuwa akan wasu kudade da suka ce ana zaftarewa daga cikin albashinsu da sunan za'a basu bashin kwamfuta amma yanzu kusan shekara guda ke nan babu labarin inda aka kwana.
Malaman sun yi tattaki zuwa ofishin Muryar Amurka dake Minna babban birnin jihar cikin bacin rai domin su mika kokansu. Kodayake basu yadda a ambaci sunayensu ba amma sun ce lamarin na daure masu kai domin kawo yanzu an yi watanni goma ana cire masu kudade. Haka ma ana sake cire wasu kudaden na basu horo akan naurar.
Sun fada a ofishin Muryar Amurka cewa sun zo ne su bayyana bacin ransu akan lamarin saboda a kowane wata ana cire ma kowa nera 2100.
Kungiyar malamai ta Najeriya wato NUT ta fada masu cewa saboda za'a basu kwamfuta ne ya sa ana cire kudin daga albashinsu. Kawo yanzu malaman sun ce an jire masu nera miliyan 147.
Babban sakataren ma'aikatar ilimin jihar Alhaji Sha'aibu Adamu yace yana da masaniya akan maganar kuma yanzu sun bada umurnin da a dakatar da cire kudaden. Shi ma sakataren yada labarai na gwamnan jihar yace lamari ne da suka gada daga gwamnatin da ta shude amma suna tattaunawa akan maganar.
Sakataren kungiyar malaman makarantu reshen jihar Neja Labaran Garba ya musanta abun da malaman ke zargi akai. Yace babu malamin da zai ce ba'a bashi horo akan anfani da kwamfuta ba.
Ga karin bayani.