Barazanar Bom: An Kara Ganin Wani Kunshin A Birnin New York

‘Yan sandan birnin New York sun sami wani kunshin sako da basu yarda da abinda ke cikinsa ba a unguwar Manhattan yau Alhamis.

Kafafen yada labarai sun ruwaito jami’an ‘yan sandan na cewa, an tura wani kunshin sako shigen irin wanda aka turawa wasu manyan ‘yan jam’iyyar Democrat a farkon makon nan zuwa wani gidan cin abinci mallakar wani shahararren dan wasan fina-finan Amurka mai suna Robert De Niro. An dai dauke kunshin a wata mota an kai shi inda za a yi nazarinsa.

Lamarin na baya-baya na zuwa ne a lokacin da masu bincike a Amurka ke kokarin gano wanda ke da hannu a aike sakonnin ababen fashewar zuwa ga wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka a yanzu da na baya, da kuma ofishin tashar talabijin ta CNN.

Shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Christopher Wray ya kira wannan binciken da hukumar ta FBI ke yi a matsayin mai matukar muhimmanci bayan da hukumomi suka gano cewa wani ya tura wasu bomabomai masu kama da bututu zuwa ga tsohon shugaban Amurka Barack Obama, da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da kuma wasu manyan ‘yan jam’iyyar Democrat.