“Abubuwa da yawa sun faru a Najeriya a wannan zaben da aka kammala. Misali, banda aikin jarida da muka samu kanmu a ciki, akwai wadanda da suka zama ‘yan jaridar dole, suna yada labarai” a cewar Mr. Keyen.
Shugaban ya kara da cewa “Abun da zan ce shine anyi gasa ne, tsakanin wadanda suka san aikin, da wadanda basu san aikin ba. Kaga kamar Muryar Amurka da yake tayi suna, dole ne a kalli aikin da tayi domin ganin irin rawar da take takawa a wannan zaben.”
“Aikin nan, yana da wuya saboda abubuwa kamar guda uku. Na daya shine, dole sai ka kware a wannan fanni na jarida, saboda kawo labaran zabe, sai ka kware a ciki. Domin yana da illa da yawa idan ba ka san aikin ba. Illoli kamar na ‘yan siyasa, su yaudare ka, su ce ‘ga wannan’ ka rufe ido ka fadi sakamakon zabe. Ka ga wannan yana nan. Na biyu, kaga wadansu ‘yan siyasa basu sonka, zasu ce kana baiwa wance dama fiye da wance, ko kana bari ana jin muryar wance fiye da wancan. Na uku akwai zancen na’ura. Kana da na’urar zamani da zaka iya yin wannan aikin da shi, ko baka da shi.
Your browser doesn’t support HTML5