Shugaban kungiyar tabital fulako reshen karamar hukumar Yola ta kudu Mal. Musa Adamu ya shaidawa muryar Amurka cewa Fulani makiyayan sukan gwammace kaura daga rugar su baya ‘yan fashin sun matsa da karbar fansa tare da yiwa rayuwarsu barazana idan sun kai koke wurin jami’an ‘yan sanda.
Yayin da kimanin barayin shanu goma zuwa goma sha biyar ake kamawa duk Laraba ranar da kasuwar Ngurore ke ci kowani mako. Dalilin da ya sa gamayyar Fulani makiyaya da mahauta suka kafa kungiyar Fulako wadda inji shugabanta Alh. Bawa Musa ya ce sun alwashin sanya kafar wando guda da barayi shanu a yankin da galibinsu sanannu ne cikin al’umarsu.
Da yake amsa tambayar ko me ya yi sanadin sake bullar ‘yan fashin baya lafawar al’amarin a ‘yan watanni da suka gabata, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Adamawa SP Othman Abubakar ya ce rashin samun bayyanai na barazanar da masu satar shanu da mutane don neman fansa daga su makiyayan, shi ya kawo koma-baya a nasarorin da suka cimma a baya.
Shima da yake bayani kan bulla barayin shanu da mutane a yankin, Aliyu Nuhu shugaban kungiyar masu sayan shanu na jihar Adamawa ya danganta yawaitar aikata miyagun laifuffuka sakanin samaran Fulani makiyaya da karuwar ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5