Duk da karancin kudi da ake kukan 'yan Najeriya suna fama da shi, hakan bai tilasta farshin dabbobi suyi kasa ba, kamar yadda bincike da kuma shiga kasuwannin suka nuna.
Wakilin Sashen Hausa a Abuja Saleh Shehu Ashaka wanda ya ziyarci daya daga cikin kasuwanni da suke babban birnin ya samu farashin raguna sun kama daga Naira 45,000 zuwa sama.
Wani dillalin dabbobi yace, banbancin kasuwar bana data bara, ya ta'allaka ne kan kudi. Bara yace akwai kudi a hanun jama'a, bana kuma babu.
Ga karin bayani.