A yayin taron shekara-shekara na kwamitin gwamnonin bankin ci gaban Musulunci karo na 48 da aka gudanar a ranar Labara, gwamnatin kasar Kamaru ta samu rancen kudi CFA biliyan 21 don sake farfado da yankunan Arewa maso Yamma da na Kudu maso Yammacin kasar.
Shugaban bankin IDB Muhmmad Al Jasser da ministan tattalin arziki, tsare-tsare da raya yankuna na Kamaru Alamine Ousmane Mey ne suka rattaba hannu a takardar rancen.
Muntary Hamisu, shugaban kungiyar farar hula kuma mazaunin Bamenda a yankin Arewa maso Yamma, ya yi farin ciki game da wannan labari. Sai dai kamar sauran mutane da yawa, Muntary Hamisu na nuna shakku kan danka wadannan makudan kudaden a hannun gwamnatin Kamaru.
Wannan rancen da aka ba kasar Kamaru, na karkashin tsarin da aka yi wa taken "Plan Présidentiel de Reconstruction et de Développement des Régions du Nord-Ouest et du Sud-Ouest", ma’ana Tsarin Shugaban kasa na sake aiwatar da gine-gine da raya yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma (PPRD).
Wadannan jihohin dai na fuskantar tashin hankali tsakanin 'yan aware masu neman 'yancin jihohin da sojojin gwamnatin Kamaru tun shekarar 2016.
Saurari rahoton Mohamed Bachir Ladan:
Your browser doesn’t support HTML5