Bankin duniya ya baiwa Najeriya rancen dala bilyan 1.5 domin baiwa gwamnatin tarayya damar aiwatar da kadan daga cikin sauye-sauyen tattalin arziki, ciki harda janye tallafin man fetur da bullo da sabbin manufofin haraji.
Hakan na zuwa ne bayan da babban bankin yace ya amince da wasu ayyuka 2: sauye-sauyen daidaita tattalin arzikin Najeriya domin bada damar sauyawa (RESET) da shirin daukar nauyin manufofin raya kasa (DPF) akan dala bilyan 1.5 sai kuma shirin hanzarta tattara kudade (ARMOR) domin haifar da sakamako (PFOR R).
Wannan kunshin na dala biliyan 2.25 ya samar da tallafin kudade domin agazawa kokarin gaggawar da Najeriya ke yi wajen daidaita tattalin arzikinta da kara tallafawa talakawa da sauran marasa galihu, a cewar sanarwar da bankin duniyar ya fitar.
Sanarwar mai dauke da kwanan wata 13 ga watan yunin 2024, tace rancen ya kara tallafawa burin da Najeriya keda shi na kara yawan harajin da take samu daga bangaren da babu ruwansa da man fetur tare da alkinta kudaden shigarta na bangaren man, da dabbaka dorewar samu da wadatuwar kudade domin aiwatar da nagartattun ayyuka ga al’umma.