A watan Afirilu, ministan kudin Najeriya Wale Edun ya ce Najeriya ta nemi lamunin kudi dala biliyan 2.25 daga bankin duniya kuma tana sa ran kwamitin gudanarwa na bankin zai amince da bukatar a watan Yuni.
A watan Mayun bara, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara daukar matakai masu tsauri na yin garambawul da ba a ga irinsu ba a cikin gwamman shekaru, inda ya cire tallafin man fetur da ke lakume makudan kudade, ya kuma dauki matakin barin naira ta nema wa kanta daraja don tada komadar tattalin arzikin kasar. To sai dai yunkurin ya haifar da mummunan tashin farashin kayayyaki da tsananin tsadar rayuwa.
A sakamakon rage darajar kudin, asusun bayar da lamuni na duniya ya yi hasashen cewa, tallafin man fetur ka iya lakume kashi 3 cikin 100 na abin da kasar za ta samu a bana.
Su ma kungiyoyin kwadago sun matsa wa Tinubu lamba kan ya janye sauye sauyen. Bankin duniya yace ya amince da bayar da lamunin dala biliyan 1.5 ne domin mara baya ga sauye sauyen da Najeriya ta yi, da kuma wasu kudi dala miliyan 750 domin zaburar da hanyoyin samar da kudaden shiga.
Bankin ya kara da cewa, Najeriya ta kama hanyar yin sauye sauye masu muhimmanci domin kawar da matsalolin tattalin arziki da karfafa hanyoyin samun kudin shigarta, ya kuma ce kasar ta dauki takun farko na muhimman matakai don maido da daidaito ta bangaren tattalin arziki, da bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga da rage talauci.
-Reuters