Bana Za Ayi A Kasar Saudiyya Babu Kasar Isra'ila

Darar Chess

Gasar hora kwakwalwa na Dara ‘chess’ a turance ta kasa-da-kasa, zai fara gudana a kasar Saudiyya, batare da samun halartar ‘yan wasan kasar Isra’il ba. A dalilin hanasu takardar visa don shiga kasar.

A cewar hukumomin kasar Saudiyya, ba zasu ba ‘yan wasan chess na kasar ta Isra’ila visa don shiga kasar ba, domin kuwa babu wata dangantakar difilomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

A cewar kungiyar darar chess ta kasar Isra’ila, zasu nemi kasar ta saudiyya da ta basu wasu kudaden ramuwa. Wannan shine karon farko da kasar ta Saudiyya ta dauki bakoncin wasan dara na duniya.

Hakan ya biyo bayan yunkurin kasar na ba sauran kasashen duniya damar shiga kasar, da kyautata dangantakar su da sauran kasashen duniya. A bangare daya kuwa, fittacciyar ‘yar wasan chess ta duniya, ta bayyanar da cewar ba zata halarci gasar ba.

Matashiya Anna Muzychuk, mai shekaru 27 da haihuwa, ‘yar asalin kasar Ukraine, ta bayyana cewar ba zata halarci gasar ba, a dalilin sai ta saka riga mai rufe mata jiki kamin ta buga wasa a kasar ta saudiyya.

Ta kara da cewar, a gaskiya koda kuwa rashin buga wasan zai sa ta rasa matsayin ta na lashe kambu 2, babu komai tafi son hakan, sarki Salman, na kasar Saudiya ya ware makudan kudade dallar Amurka $750,000, kimanin Naira milliyan dari biyu da saba’in ga duk wanda ya lashe wasan.