Bana-Bakwai

Bana Bakwai

Shirin bana bakwai na wannan makon ya ji irin sababbin kalmomin da matasa kan yi anfani da su a zamanance domin bayyana ra'ayi ko isar da wani sako ga abokan su ne, dan haka shirin ya ziyarci jahar Zamfa da Kebbi sa'an nan muka koma Nasarawa.

Kamar yadda wani matashi daga jahar Kebbi ya ce idan kaji matashi yace "masga" to yana nufin aikata abu mara kyau kokuma wani ya fadi karya, haka kuma duk inda kaji matashi ya ce "cika" manufar anan itace budurwa.

A jahar Nasarawa kuma idan kaji matasa sun ce "wani ya ci abinci da rana wato suna nufin yayi abin kunya kenan.

Saurari cikakken shirin a nan...Dandalinvoa.com