Ban-Ki-moon Yayi Tur da Mamaye Ofishin Hukumar Zaben Gambia da Sojoji Suka Yi

Ban Ki-moon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD da zai cika wa'adinsa karshen watan nan

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da kwace hukumar zaben kasar Gambia da jami’an tsaron kasar suka yi kuma ya yi kira garesu da su fice daga ginin na da nan.

A wata sanarwar da kakakin babban sakataren ya fitar jiya Laraba, shugaban na MDD ya yi kira ga sojojin Gambia da kada su aikata wani abin da zai iya jefa zaman lafiyar kasar cikin rudani a shirin mika mulki da ake ciki a kasar ta Afrika ta Yamma.

Wata tawagar shugabannin Afrika ta Yamma da ta kunshi mutane hudu karkashin jagorancin shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta gana da shugaba Jammeh a shekaran jiya Talata a Gambia.

Bayan ta dawo shugaba Johnson Sirleaf tace bangarorin gwamnati da na ‘yan adawa duk sun amince da tattaunawar zaman lafiya, a don haka tace za’a ci gaba da tattaunawar a taron koli na kasashen ECOWAS da za’a yi a karshen wannan mako a birnin Abujan Nigeria.