Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya nuna damuwa kan ambaton sunansa da Shugaba Bola Tinubu ya yi a cikin sanawarsa game da lalata sakatariyoyin kananan hukumomi a jihar.
Fubara ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na Channels a shirin “Politics Today” a ranar Litinin.
A ranar Asabar aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar inda jam’iyyar Action Peoples’ Party (APP) ta lashe kananan hukumomi 22 cikin 23 yayin da jam’iyyar Action Alliance (AA) ta lashe kujera daya.
Jam’iyyun APC da PDP sun kauracewa zaben.
A ranar Lahadi Gwamna Fubara ya rantsar da duka shugabannin kananan hukumomin sai dai an kai hari kan wasu daga cikinsu yayin da suka yi yunkurin kama aiki a kananan hukumomin.
Kazalika an banka wuta a sakatariyoyin wasu daga cikin kananan hukumomin.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ta hannun Kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya kama sunan Fubara inda ya yi kira a gare shi da "shugabannin siysar jihar " da su tabbatar da doka da oda, kalaman da ba su yi wa Fubara dadi ba.
“Ba ni da wata matsala (tsakanina da Shugaban kasa), amma ina da dan damuwa lokacin da aka ambaci sunana kawai.
“Lamarin yana da sauki sosai. Yana da sauki kamar ABC, kowa a Najeriya, kowa a Jihar Ribas ya san inda wannan matsalar take fitowa. Ba wani abu ne mai wahala ba. Muna sane da mece ce matsalar, kuma matsalar ba Fubara ba ce, ba haka ba ne." Fubari ya ce.