A cikin wata sanarwa daga mataimaki na musamman na shugaban kasa akan sha’anin watsa labarai Malam Garba Shehu, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba za’a lamincewa hare-haren ta’addanci da ake kai wa al’ummomi a jihar, da kuma na baya-bayan nan wanda aka kai wa gwamnan jihar kan sa ba.
Shugaban kasar ya kuma jinjinawa rundunar ‘yan sanda akan aikewa da tawagar kwararrun masu bincike a jihar, inda kuma yayi kira gare su da su yi kokarin bankado dukan masu hannu a kai harin, da kuma hukunta su.
Karin bayani akan: PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.
Bayan jajantawa gwamnati da al’ummar jihar akan lamarin, shugaba Buhari ya yi kiran da kada a sanya siyasa a kan lamarin, inda ya jaddada cewa “kai hari akan dan Najeriya daya, tamkar kai hari ne ga dukan ‘yan kasar.”
A ranar Assabar ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan kwamban motocin gwamnan na jihar Benue Samuel Ortom, a kan titin Makurdi zuwa Gboko, sa’adda ya ke kan hanyar ziyartar gona a Tyo.
Ku Duba Wannan Ma ‘Yan Bindiga Sun Kai wa Gwamnan Benue Samuel Ortom HariTuni dai da kungiyar gwamnonin Arewa suka jajantawa takwaran na su akan lamarin, inda kuma suka dau alkawarin daukar mataki akai.
Ku Duba Wannan Ma Hari Kan Gwamna Ortom: Gwamnonin Jihohin Arewa Sun Dauki MatakiA bangare daya kuma kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya, sun yi tir da kakkausar murya, da harin da aka kai kan gwamnan na jihar Benue.
Wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin na PDP, kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, sun bayyana harin a matsayin “wani yunkuri na hallaka gwamna Ortom.”
Haka kuma gwamnonin sun bayyana cewa “duk wani yunkuri na cutar da daya daga cikin mu, tamkar yunkuri ne na cutar da mu baki daya.”
Gwamnonin na PDP sun yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta kara mai da hankali wajen tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayin su a cikin al’umma ba.
Ku Duba Wannan Ma Ba Za Mu Amince Da Kai Hari Akan Dayanmu Ba - Gwamnonin Najeriya