Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Amince Da Kai Hari Akan Dayanmu Ba - Gwamnonin Najeriya


Shugaban kungiyar NGF, Dr Kayode Fayemi na jihar Ekiti
Shugaban kungiyar NGF, Dr Kayode Fayemi na jihar Ekiti

Gwamnonin Najeriya, sun mayar da martani da kakkausar murya kan harin da aka kai akan takwaran aikinsu na Benue, Samuel Ortom.

Kungiyar gwamnonin Najeriya, ta yi Allah wadai da wani hari da aka kai akan gwamnan jihar Benue Dr. Samuel Ortom, wanda suka kwatanta a matsayin abin ban-tsoro da takaici.

A ranar Asabar wasu 'yan bindiga suka kai harin akan gwamna Ortom yayin da yake rangadin gonarsa da ke hanyar Gboko.

Karin bayani akan: Fulani, Shugaba Muhammadu Buhari​, jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.

Shugaban kungiyar, kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter.

A cewar gwamna Fayemi, dole a taru baki daya a tashi tsaye don gano wadanda ke aikata wannan mummunan aikin.

Kungiyar ta kara da cewar “hari da aka kai akan gwamnan Samuel Ortom, hari ne da ba za’a amince da shi ba, kuma masu harin ba za su taba yin nasara ba.”

Sanarwar ta kara da cewar “Kungiyar mai gwamnoni 36, za ta ci gaba da karfafa gwiwa ga mambobinta, tare da kira a gare da kada su yi kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukansu da jama’a suka zabe su yi.”

“Ba za’a bar ta’addaci ya rufe ayyuka na gari ba, ba dai a jihar Benue ko a duk fadin kasar ba.”

Gwamna Fayemi ya kara da cewar sauran gwamnoni za su ci gaba da yi wa Dr. Samuel Ortom addu’a, kuma ba za su sake yin nasara ba, da kuma fatar za’a kama su nan gaba.

Yayin wani taron manama labarai da ya yi bayan faruwar lamarin, Gwamna Samuel Ortom ya ce ya yi gudun tsira da ransa na kimanin kilomita daya da rabi, da taimakon jami’an tsaronsa Allah ya kubutar da shi, yana mai cewa ya wannan hari, Fulani ne suka kai mishi.

Ya kuma daura laifin duk hare-hare da ake kai wa akan kungiyar Miyyeti Allah, da cewar ita ke haifar da wannan ayyukan ta’addancin.

Kokarin jin ta bakin kungiyar ta Miyetti Allah ya cutura domin wasu daga cikin shugabannin kungiyar sun ce ba su da abin fada kan wannan lamari.

Sai dai gwamnan na jihar Benue ya ce lauyoyinsa za su kalubalanci kungiyar, don haka ya yi kira da a yi bincike na gaske, don yana ganin cewar akwai Fulani da ke fitowa daga wasu kasashe makwabtan Najeriya, suke aikata wannan ta’asar.

Akan batun filin kiwo ga Fulani, ya kara jaddada cewar suna nan akan bakarsu ta hana kiwo a jihar, don ya tuntubi jama’a jihar sun nuna ba sa bukatar hakan. Idan kuwa har za’a bukaci yin gyara akan kundin to za’a samar da tsauraran matakai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG