Bamu Fadi Ba – inji ‘Yan PDP

Godsday Orubebe na Jam'iyyar PDP.

Yayin da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ke shirye-shiryen mika mulki ga shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan gobe na Mayu, Jam’iyyar PDP ta shugaba mai barin gado tace ta daura damarar yin hamayya mai karfi ga sabuwar gwamnatin APC a kasar.

A hirarsu da wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari a Kano, mataimakin shugaban PDP na kasa mai kula da shiyyar arewa maso yammacin najeriya Ambasada Ibrahim Kazaure yace zasu ci gaba da zama a cikin Jam’iyyar ba zasu bar ta ba.

“Muna nan a PDP, daram-dam. Babu wani abu da yake bamu tsoro. Domin siyasa ma yanzu aka fara. Wadanda ba ‘yan siyasa ba, su zasu gudu” inji Mr. Kazaure.

Amma jam’iyyar PDP ta share shekaru 16 tana mulkin kasa.

“idan aka duba tarihi, mace ba ta sanin miji na gari, sai ta auri maza biyu. Yanzu Najeriya ta yi aure na biyu. Yanzu na Najeriya za ta san, za’a yi siyasa”.

Wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari ya tambayi Ambasada Kazaure ko meyasa ba’a la’akari irin ayyukan da jam’iyyar tayi ba, domin a kara zabar ta.

“Mu bamu fadi ba, muna nan a Jigawa, domin babu dan PDP na Jigawa da ya fita.”

Your browser doesn’t support HTML5

Bamu Fadi Ba – inji ‘Yan PDP – 3’10”