Yanzu haka gwamnatin jahar Barno ta kuma dibar 'yan gudun hijirar bayan tsaikon da aka samu na rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jahar Alhaji Zanna Mustapha.
A cewar wata matar da bata bayyana sunan ta ba, ta ce "mun fito ne daga kamaru kuma ina mai matukar farin cikin komawa gida, jiya ko bacci ban yi ba saboda farin ciki".
Ko me jama'ar jahar Bornon ke cewa dangane da abin da ya faru a sansanin 'yan gudun hijirar da kuma wannan mataki da gwamnatin jahar ta dauka a yanzu?.
Alhaji Abdulrashid Maina BIiyu da ke zama tsohon shugaban kwamitin inganta sha'anin fansho a Najeriya ya yaba kwarai dangane da matakin da gwamnan jahar ya dauka.
Tsohon shugaban ya kara da cewa "da farko dai ina mai tausayawa 'yan uwan wadanda suka srasa rayukan su a wannan tashin tashin bam, da kuma mutane ashirin da suka jikata, bayan haka kuma muna mika mgaodiya ta musamman ga gwamnan jahar musamman yadda ya ke daukar dawainiyar wadannan mutane, dan haka mun gode kwarai".
Daga karshe ya ce lallai kokarin da ake na tabbatar da ganin sun koma gidajen su zai ci gaba, ya kuma kara da cewar an kara daukar tsauraran matakan tsaro a dukan sansanin da ke fadin jahar domin kaucewa sake afkuwar irin wannan matsala.
Saurari karin Bayani.
Your browser doesn’t support HTML5