Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Furuci Akan Makaman da Rasha Take Turawa Syria


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, ya yi magana da takwaran aikinsa na Rasha Sergei lavrov,kan makamai da Rasha ke turawa Syria

Ana ganin kwararar makamai daga Rasha zuwa Syria da zai kara sa rikicin da ake yi a kasar ya kara tsanani.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta fada cewa hukumomin Rasha suna kafa wani sansanin mayakan sama kusa da birnin Latakia mai tashar jiragen ruwa, dake arewa maso yammacin kasar.

A taro da manema labarai da yake yi a ko wace rana, kakakin fadar White House ta shugaban Amurka, Josh Earnest, ya sake nanata matsayin Amurka cewa, goyon bayan da Rasha take baiwa shugaban Syria Bashar al-Assad "adashi ne da Rashar ba zata diba ba".

Earnest ya ce ta yiwu shugaba Obama ya kira tawakaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Wata jaridar Rasha mai suna "Vedomosti", ta ambaci wata majiya kusa da ma'aikatar tsaron Rasha a cikin wani rahoto data buga jiya Talata cewa, abunda Rasha take yi shine gyara da kuma taimakawa wajen tabbatar da lafiyar kayan aiki a sansanin mayakan saman dake Latakia.

Amma masu lura da al'amarun yau da kullum a Moscow, sun ce abunda jami'an Rasha wadanda suke Syria suke yi ya zarce gyare-gyare da horasda jami'an tsaro na kasar Sham din.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG