Gwamnatin shugaba Trump tace hukumcin da wani alkali ya yanke da ya umaraci gwamnati ta sada iyaye bakin haure da ‘ya’yansu wadanda aka raba a kan iyakar kasar Amurka zai sa a tsare kananan yaran a na lokaci mai tsawo fiye da yadda ake yi a halin yanzu.
Ma’aikatar shari’a ta bayyana a cikin wata takarda da ta shigar a kotu jiya jumma’a cewa, “gwamnati ba zata raba iyalai ba, amma zata tsare su tare a lokacin da ake tantancesu bayan an kamasu suna kokarin keta kan iyaka zuwa Amurka.
Yana yiwuwa a tsare iyalai na tsawon watanni ko ma shekaru sabili da dubban takardun bakin hauren da suke jibge a kotu da ba a samu kaiwa garesu ba sabili da yawansu.
Wata dokar kotu da ake kira yarjejeniyar Flore ta hana a tsare kananan yara fiye da kwanaki ishirin.
Alkalin wata kotun Amurka a birnin San Diego na jihar California ya yanke hukumci cewa, tilas ne a gama iyayalan da aka raba cikin kwanaki talatin, a kuma maida kananan yara ga iyensu cikin makonni biyu.
Jami’ai sunce kimanin kananan yara dubu biyu ne suke jira a gamasu da iyayensu