Bakin Haure 43 Sun Rasa Rayukansu A Wani Hadarin Kwale-kwale A Tekun Italiya

Deadly migrants boat accident off Italy coast

Akalla bakin haure 43 ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwalen katako da suka yi cunkoso a ciki ya daki wasu duwatsun ruwa, ya kuma balle a kudancin Italiya kafin wayewar gari ranar Lahadi, in ji jami’an tsaron gabar tekun Italiya.

WASHINGTON, D.C. - An bayar da rahoton cewa wadanda suka tsira da ransu sun nuna cewa wasu da dama na iya bata a cikin ruwan.

“Ya zuwa yanzu, an ceto mutum 80 da ransu, wasu daga cikinsu sun yi nasarar tsira bayan da jirgin ya kife, amma an gano gawarwakin mutum 43 a gabar tekun,” in ji jami’an tsaron gabar tekun a wata sanarwa da suka fitar jim kadan da tsakar rana.

Daga baya gidan talabijin na kasar Italiya ya ba da rahoton cewa an kawo gawarwakin mutum 45 da aka lullube da mayafi zuwa filin wasanni a birni mafi kusa na Crotone.

Haka kuma an yi kiyasin mutane da yawa ne a cikin kwale-kwalen a lokacin da ya yi karo da duwatsu da igiyar ruwa.

Rahotanni daga kauyen Steccato di Cutro, gidan talabijin na kasar ya nuna wadanda suka tsira da rayukansu na cewa jirgin ya tashi ne kwanaki biyar da suka gabata daga Turkiyya dauke da fasinjoji sama da 200.

Jami'an tsaron gabar tekun Italiya, wadanda ke gudanar da aikin ceto, sun ce kimanin bakin haure 120 ne ake kyautata zaton suna cikin jirgin.

-AP