Dan wasan Barcelona Lionel Messi na ci gaba da jan zarensa, a fagen tamola inda ya yi ta kafa tarihin da babu kamarsa.
Domin babu wanda ya taba ci wa Barcelona kwallaye har guda (566) kamarsa, Messi ya zura kwallo (392) a wasan La Liga yayin da ya ci wa kasar Argentina kwallo (65), inda ya kasance gwarzon dan kwallon Duniya
na FIFA sau biyar sannan ya dauki kofi a Kungiyar Barcelona sau 33.
Dan wasan mai shekaru 31, da haihuwa har yanzu bai nuna alamar gajiya ba, a bana Messi ya zura kwallaye 14 a wasa 13 na dukkan gasar da ya fafata, sannan ya bi sahun manyan 'yan wasan da suka fi zura kwallo a gasar La Liga.
Inda yake cin kwallo daya a duk minti 87 duk da cewa makonsa uku bai buga wasa ba sakamakon karayar da ya samu a hannunsa.
Ku Duba Wannan Ma Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Duniya Sun Shiga Riga DayaYa yi wasa a karkashin shugabancin manajoji shida a Nou Camp, kuma
yanzu shi ne kyaftin din kulob din bayan Andres Lniesta da ya bar Kungiyar.
Hakan na nuna irin tasirin da Messi ke da shi a Nou Camp, domin kuwa ko da manajansa Ernesto Valverde ya yi amannar cewa dan wasan ya fi shi sanin abin da ya kamata a yi.
Messi yana hutu daga buga wa kasarsa Argentina wasa, bayan da ya gaza ciyo mata wani babban kofi, Kwantarakinsa a Barcelona zata kare a shekara ta 2021, kuma ya ce ba zai iya buga wa wani kulob wasa ba sai tsohowar kulob dinsa na Boyhood Club Newell's Old Boys.