Bai Kyautu Ayi Gasar Kwallon Kafa na Duniya a Kasar da Bata da Tarihin Kwallon Kafa ba

Filin wasa a Qatar

Shahararren tsohon dan wasan kwallon kafa dan kasar Brazil, Zico, yace bai kamata a baiwa kasar da bata harkar kwallon kafa , nauyin gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ba.

Yace bai kamata a gudanar da gasar a kasar Qatar ba, domin tsegume-tsegume da akeyi cewa akwai al’mun cewa an bada cin hanci kafin a tabbatar wa Qatar gudanar da gasar na shekarar 2022.

Ya kara da cewa koda yake Qatar kasar ce dake tasowa amma bai kyautu ace za’ayi irin wannan gagarumin wasa a kasar da bata tarihin kwallon kafa ba.

Zico, yace “na san Qatar lokacin da nake Koch din kasar Iraqi, ba’a samu mutane 1000 daya a filin wasa idan ana kwallo, wasu wasanin ma ko ‘yan uwan ‘yan wasan ma basu zuwa.”