Bai Kamata Shugaban Al'umma Ya Zama Makaryaci, Maras Kunya Ba - In Ji Gwamna Yari

Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya

Gwamnan Jihar Zamfara yana mayarda martani ga batun korar wasu jami'an gwamnati da kuma ikirarin ministan labarai cewa jihohi sune ba su yin abubuwan da suka kamata
Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, yace bai kamata a ce shugaban al'umma ya kasance makaryaci kuma maras kunya ba. Gwamnan yana mayarda martani ne ga kalamun da aka ji daga bakin ministan labaran Najeriya, Labaran Maku, wanda ya kare zargin handame dubban miliyoyin daloli da ake wa kamfanin man Najeriya da cewa ita gwamnatin tarayya tana yin abinda ya kamata, jihohi ne ba su yi.

Gwamnan na Zamfara, yace saukar ministoci da jami'in ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka yi, ba ita ce matsalar Najeriya ba, matsalar ita ce batun dubban miliyoyin dalolin da suka bace, ko sama ko kasa, sai kame-kame ake yi a kansu.

Gwamna Yari yace a irin wannan lamarin, su manyan jami'an gwamnatin da suke da hannu a wannan abu ne ma ya kamata su yi ma kawunansu qiyamul laili, su sauka daga kan mulkin, maimakon su zauna su na ta kame-kamen yadda aka yi da wannan kudi.

Haka kuma, gwamnan na Zamfara ya kalubalanci masu kare irin mummunan warwason dukiyar jama'a da ake yi a gwamnatin tarayya, warwason da yace su da kansu jami'an gwamnatin suke fadawa duniya, da su zo su bayyana abinda suka ce ana yi a jihohin irinsu Zamfara.

Yace sau da dama hukumomin yaki da zarmiya da cin hanci na gwamnatin tarayya a Najeriya su na gayyatar wasu jami'an gwamnatin Zamfara da su amsa tambayoyi kan wasu kudaden da ake zargin wai an yi ba daidai da su ba, amma ko da sau daya ba su taba samun wani da aka ce ya aikata laifi ko satar wani abu ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Abdulazeez Abubakar Yari na Zamfara ya Shawarci Mahandama a Gwamnatin Jonathan - 4:12