Da ma kwararru a fannin zamantakewar al'umma sun ce rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa, yana daya daga cikin abubuwan dake haddasawa da kuma rura wutar tashe-tashen hankula.
Kwamishinar yaki da talauci a jihar Borno, Dr. Zainab Kyari Gimba, ta fadawa wakiliyar Muryar Amurka, Sa'adatu Mohammed, cewa sun samu nasarar cimma kashi 90 cikin 100 na gurinsu na samarwa da matasa ayyukan yi, musamman a cikin Maiduguri, babban birnin jihar.
Ta ce har a wasu garuruwa na jihar ma, sun samu nasarar samarwa da matasa da mata ayyukan yi, tare da koyar musu sana'o'i dabam dabam da zasu sanya su zamo masu dogaro da kai.
Dr. Kyari Gimba, ta ce matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Jihar Borno da wasu makwabtanta, ita ce ma ta hana su cimma kashi 100 bisa 100 na wannan guri nasu.
Ga cikakken rahoton da Sa'adatu Mohammed ta aiko daga Maiduguri.