Kawo yanzu ma'aikatar shari'a ta Neja ta tabbatar da samun takardu bayanan da ake bukata daga 'yan sandan Kontagora garin da aka yiwa Aisha Rabiu fyade domin fara shari'a gadan gadan. Da yake tabbatar da samun takardun Malam Muazu Shehu darakta a sashen manyan laifufuka na ma'aikatar shari'a yace "Halin da muke ciki Malam Batsari 'yan sanda jiya suka kawo mana file na yarinyar. Ga procedure namu mu nan zamu karantashi mu ga shedun dake ciki takamamme ne wanda yake ya isa za'a iya hukunta wannan yaran ko ko babu. To a yanzu mun riga mun duba kuma shedun dake cikin file din sun nuna mana cewa kwararrun shedu ne wanda yake ana iya gabatar da hukunci a kan wannan yaran. Isha allahu abun da ya kama daga Talata zuwa Laraba zamu shiga kotu" Kamar yadda ya kara yana nufin makon gobe.
Dangane da korafin da mutane keyi cewa shari'a tana samun jinkiri sai Malam Muazu Shehu yace da yadda Allah ba za'a samu jinkiri ba domin mahimmancin da suka ba maganar. Ya kara da cewa idan an kawo masu file su kan dauki mako biyu ko uku kafin su yanke shawarar ko su je kotu ko su yi watsi da maganar. Amma wannan da suka samu takardun nan take suka karanta suka kuma yanke shawara.
Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar ita yarinyar wanda shi ma lauya ne Sanata Ibrahim Musa yace lamarin ya bata masa rai kuma zasu sa ido su ga yadda zata kaya.Yace "Na samu labarin wannan abun, ban jishi ba sai a rediyo. Wannan abun bai yi dadi ba ko kadan. Irin wannan dabi'a ya kamata iyaye su yi ma yaransu gargadi wannan dabi'a a barshi. Bai yi dadi ba kuma ina rokon hukuma da su dauki mataki kwarai da gaske kan yaran da suka yi wannan abun. Babu maganar cewa ni dan gidan wani ne ko dan gidan wance. Kuma zamu sa ido mu gani. Idan wani abu ya taso don a hana hukunci zamu sa baki ciki...Idan aka ce za'a yi wani abu a matsayinmu na masu wakiltar mutane zamu tashi tsaye"
Bayan Aisha ta kwashe kusan wata guda a asibiti yanzu an sallameta sabili da samun saukin da ta yi.