Bai Kamata Kananan Yara 'Kasa Da Shekara Daya Su Sha Leman Kwaba Ba

Wani rahoto da aka buga a mujallar aikin jinyar kananan yara ya shawarci cewa, bai kamata a ba kananan yara kasa da shekara daya ruwan lemun kwalba ba, sai da izinin likita, kamata ya yi a ba kananan yara ruwan nono ko kuma madarar jarirai.

Wannan ne karon farko tun shekara ta dubu biyu da daya da kungiyar likitocin ta sake nazarin shawararta kan lemun kwalba, wanda yake kan gaba a jerin hanyoyin da ake samun sukari daga abinci.

Likitocin sunce bai kamata kananan yara tsakanin shekara daya zuwa hudu su kwankwadi ruwan lemun kwalba da ya wuce milimita dari da goma sha takwas ba.

Binciken yace ana iya ba kananan yara abin sha na kwalba dangin lemu da ba a surka da komi ba, sai dai kada a basu lemun kwalban fiye da sau biyu a wuni.

Kungiyar likitocin ta kada ta rika ba kananan yara lemun a cikin kwalba da zasu rika zuka dukan wuni ba domin zai iya bata masu hakori, a maimakon haka sun bada shawara a ba yara lemu a cup su shanye a lokaci daya.