Bai Kamata Duk Dan Bindiga Ya Ci Gaba Da Rayuwa Ba - El-Rufai

  • Murtala Sanyinna

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ba wani dan bindiga da ya kamata ya ci gaba da rayuwa, kuma wannan ne makomar duk ‘yan ta da kayar baya a jihar.

A yayin da yake bayani a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, Gwamna ​Nasir El-Rufai ya aminta cewa ayukan ‘yan bindiga da suka hada da kai hare-hare, kisan jama’a da satar mutane sun kara uzzura a jihar ne, sakamakon matsayar da ya yi na cewa ba zai yi sulhu da ‘yan ta’adda ba.

To sai dai gwamnan ya kara jaddada cewa “ba zai yiwu mu dauku kudin jama’a mu baiwa ‘yan ta’adda ba, kuma duk dan ta’addar da ya shiga Kaduna da mugun nufi na ta’addanci, to karshensa mutuwa ne.”

Karin bayani akan: ​Nasir El-Rufai, Channels, Kaduna, Nigeria, da Najeriya

El-Rufai ya ce ya yi amanna cewa babbar mafita akan matsalar tsaro shi ne karfafa ayukan soji ta sama da kasa, ta yadda za su damar kawar da dukan ‘yan ta da kayar baya.

Gwamnan Kaduna a yayin karbar mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun 'yan bindiga.

“Ai muna ganin abinda ke faruwa a jihohin Nasarawa, Kaduna, Naija da Zamfara, inda sabon babban hafsan sojin saman Najeriya ya ci gaba da luguden wuta akan ‘yan bindigar, ga su nan suna gudun tsira da rayukansu” in ji gwamnan na Kaduna.

Da wannan, ya bayyana yakinin cewa za’a iya murkushe ayukan ta’addancin nan da ‘yan makwanni masu zuwa, tare da hadin gwiwa da aiki tare tsakanin ‘yan sanda da sojoji.

Jihar ta Kaduna dai ta fuskanci ayukan ‘yan bindiga a ‘yan makwannin nan, da suka hada da kai hare-hare da kisan jama’a, satar mutane ciki har da ma’aikata da dalibai, lamarin da ake ta’allakawa da furucin na gwamnan cewa ba zai yi sulhu da ‘yan bindiga ba.

Ko a makwanni biyu da suka gabata ma iyayen daliban kwalejin koyon aikin gona da gandun daji ta Kaduna, sun yi wata zanga-zangar neman a sako yaransu da har yanzu suke a hannun ‘yan bindiga.

Rescued Abducted Kaduna school Children.

To sai dai da yake maida martani akan lamarin, gwamna El-Rufai ya ce yadda ake son gwamnati ta biya kudin fansa domin a sako yaran kan iya haifar da illa ga jihar.

“Muna jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu, to amma ba maslaha ba ne a ba da fifikon ga bukatunku kadai fiye da na daukacin al’ummar jihar ba,” in ji Nasir El-Rufai.