Janar Yakubu Gawon yace, “su zargi sojan Najeriya wannan ba dai dai bane, domin ba’a taba horas da sojan Najeriya suyi hakan ba, bai kamata suyi wannan zargi ba, wannan ba dai dai bane don haka su neman gafarar rundunar sojan Najeriya, dama Najeriyar.”
A nasa bangaren babban hafsan Najeriya, laftanar Janaral Tukur Buritai, yace kwanannan shugaban kasa ya amince da wasu kudade da za’a sayo wasu karin manyan makamai, ya kuma ce cikin wa’adin watanni ukun da aka baiwa sojan Najeriya su kawo karshen ‘yan Boko Haram, ya zuwa yanzu anyi nisa sosai kuma za’a cimma wa’adin kafin ma lokacin ya kare.
Tunda farko dai sai da sakatare da dindindin na ma’aikatar tsaron Najeriya, Isma’ila Aliyu yace, “Alamu duk sun tabbatar da za’a cimma wa’adin kawo karshen ‘yan Boko Haram, kamar yadda shugaban kasa yake da muradi.”
Saurari Cikakken Rahotan