Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dauki Tsauraran Matakan Tsaro a Manyan Masallatan Jihar Taraba


Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya
Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya

Bisa ga rahotannin siri da jami'an tsaro suke dashi sun dauki tsauraran matakan tsaro a manyan masallatan jihar Taraba domin tabbatar da ba'a samu aukuwar ta'adanci ba

An tura jami'an tsaro zuwa masallatan idi dake manyan biranen jihar domin kare rayukan masallata.

Amma an kira jama'a da su sa ido a masallatan da suke saboda gano duk wani da basu yadda dashi ba. Haka ma jama'a su lura da wuraren hada-hadar jama'a.

Daukan matakan tsaron nada nasaba da rahotannin sirin da hukumomin tsaro ke cewa sun samu game da barazanar kai hari ko kunar bakin wake a masallatai musamman a wuraren hada-hadar jama'a.

Saidai hukumomin tsaro sun bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu amma su sa ido akan kawo komo da jama'a keyi da zummar ba jami'an tsaro rahoton abun da basu yadda dashi ba.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Joseph Kwaji ya bayyana irin matakan da suka dauka game da bukuwan sallan. Yace akwai jami'an tsaro da zasu tabbatar an yi sallah lafiya.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG