Badaru Ya Maida Martani Kan Rahoton Ambaliyar Ruwa a Hadejia

Gwamnatin jihar Jigawa a Najeriya tace tana dakon shawarwarin kwararru akan rahotan da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa, inda ta bukaci mahukunta su sauyawa garin Hadejia matsugunni saboda barazanar ambaliyar ruwa da garin fuskanta a kowace shekara.

Rahotan binciken wanda kwamitin kwararru akan sauyin yanayi da sha’anin muhalli, karkashin kulawar majalisar dinkin duniya suka fitar, ya yi hasashen cewa, ambaliyar ruwa za ta mamaye garin Hadejia baki dayansa nan da shekaru biyu masu zuwa.

Don haka, akwai bukatar mahukunta su dauki matakin sauyawa Hadejia matsugunni domin kare rayuwa da dukiyar al’umma.

Hasashen kwararrun wanda aka yi amfani da hanyoyin kimiyyar fasahar zamani, ya nuna su-ma garuruwan Auyo da Birniwa da ke makwaftaka da garin na Hadejia na cikin yanayin barazanar mamaya daga ambaliyar ruwa.

Rahotan ya lura da tsananin ambaliyar da ta wakana a Hadeija a bara da-ma sauran garuruwa da ke kan hanyar Kogin Hadejia-Jama’are da kuma Komadugu zuwa tafkin Chadi.

Karin bayani akan: gwamna Badaru Abubakar, Hadejia, Majalisar Dinkin Duniya, tafkin Chadi, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai a karon farko gwamna Badaru Abubakar ya magantu dangane da wannan rahoto.

A wata gajeriyar kasida da ya wallafa game da rahotan Majalisar Dinkin Duniya akan makomar Hadejia, Arch. Aminu Kani ya ce, daukar matakan kare Hadejia daga barazanar ambaliyar ita ce mafita amma ba sauyawa garin matsuguni ba, la’akkari da dinbin kayan al’adu da kadarorin gwamnati da na daidaikun mutane na biliyoyin naira a garin Hadejia.

Sai dai gwamna Badaru Abubakar na cewa, ko da yake batu ne na amfani da ilimin kimiyya, amma lissafin kalkuleta ne zai fayyace matakin da gwamnati za ta dauka bayan karbar rahotan kwararru akan wannan lamari.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Badaru Ya Maida Martani Ga Majalisar Dinkin Duniya Kan Rahoton Ambaliya a Hadijia