Kungiyar kwadago a jihar Gombe, ta jinjinawa Gwamna jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo, a bisa kokorinsa na ganin cewa ma’aikatan jihar da masu karban fansho suna karban hakkokinsu akan lokaci batare da wani jinkiri ba.
Gwamnan yace “shi kam ma’aikatan jihar basu binshi bashin albashi, babu wani hikima babba sai dai tattali na gaskiya, kuma daga yadda muke ganin shugowar kudi daga Gwamnatin tarayya ina ganin nan bada dadewa ba duk iya hikiman mutun idan bai maida hakali sosai kuma yasa ido akan kudade da zasu shigo ba to ina ganin kowace irin Gwamnati har ta tarayya zata iya samun matsaloli ta yadda za’a tafiyar da kudi a nan gaba domin na fahimci haka kuma na fara daukar mataki na ganin cewa ban shiga irin wadannan matsaloli zuwa gaba ba.”
Shugaban kungiyar kwadago na jihar Gombe Haruna Kamara, yace Gwamna Dankwambo, yayi fice kan biyan hakokin ma’aikata akan kari yana mai cewa 25 zuwa 30 ga wata kowane ma’aikaci ko kuma mai karban fansho sun samu kudinsu a jihar Gombe.