Babu Tsaro a Guruwan Da Aka Kwato - Monguno

Garin Dikwa da sojojin Chadi suka kwato daga hanun'yan Boko Haram.

A jihar Borno mutane na korafin rashin cikakken tsaro a garuruwan da dakarun hadin gwiwa suka kwato daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram.

Rahotanni daga Jihar Borno na cewa, babu tsaro a garuruwan da aka kwato daga hanun ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Dan Majalisar Wakilai daga jihar, Muhammad Tahir Monguno ne ya bayyana haka, a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

Garuruwan da dama sun komo hanun dakarun Najeriya da taimakon dakarun hadin gwiwa daga kasashen Chadi da Kamaru da Nijar a ‘yan kwanakin nan inda aka kwato garuruwa irinsu Dikwa da Damasak da Gamboru da Monguno da kuma Bama.

“Babbar matsalar da ake samu yanzu ita ce kananan hukkomomin nan, wato manyan-manya garuruwa sojojin suke, su ‘yan Boko Haram da ba a samu an kashe su ba yawanci sun koma kauyuka na kananan hukumomin, babbar matsalar da ake ciki ke nan.”

A makon da ya gabata ne, dakarun Chadi suka kwato garin Gamboru amma bayan ficewarsu sai wasu mahara sukai kai hari garin suka kasha mutane da dama.

Hakan dai na faruwa ne yayin da kasar ta Najeriya ke fuskantar manyan zabuka a ranar 28 ga wannan wata na Maris.

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Tsaro a Gauruwan Da Aka Kwato - Monguno- 3'55"