Babu Masu Kada Kuri'a - In ji Masu Sa Ido

Mazabar "Tarauni Gardens" a Kano ana tantance sunayen masu zabe kafin su fara jefa kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin tarayya

A mafi yawan jihohi an samu inganci kan yadda aka gudanar da zabuka musamman ma ta fannin isar kayayyaki akan kari da kuma na'urar tantance masu zabe, sai dai an samu karancin masu zuwa kada kuri'u.

Bayan da aka kammala zaben gwamnoni a wasu jihohi a Najeriya, wasu daga cikin kungiyoyi da jam’iyyu da ke sa ido a zaben, sun ce hukumar zaben kasar ta INEC ta gyara kurakuran da aka yi a zaben shugaban kasa.

Masu sa idon sun kuma ce sun gamsu da irin yadda aka gudanar da zaben a wurare da dama domin ba a samu cikas ba.

Sai dai a wurare da dama, masu sa ido sun ce an samu karancin fitowar masu kada kuri’a a wannan zabe na gwamnoni.

“Gaskiya a wurare da dama mutane ba su fito ba domin mun zagaya wurare da dama, amma ban san dai yadda yankunan karkara su ke ba, amma a cikin gari babu jama’a da dama.” In ji Sanusi Inuwa Mai Gado, daya daga cikin masu sa ido a zaben jihar Pilato.

A cewar Mai Gado dalilin da ya sa ya ke ganin aka ki fita, shi ne “mutane a nasu tunanin sun samu biyan bukata a zaben shugaban kasa,saboda babu ruwansu da zaben gwamnoni jihohi.”

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Masu Kada Kuri'a - In Ji Masu Sa Ido - 1'51"