Babu Duriyar Daliban Chibok - Sojin Najeriya

'Yan matan Chibok da aka sace a ranar 14 ga watan shekarar 2015

Duk da cewa yankuna da dama ya komo hanun dakarun Najeriya a fadan da su ke yi da Boko Haram, hukumomi sun ce har yanzu babu duriyar 'yan matan Chibok.

Dakarun Najeriya sun ce har yanzu babu doriyar dalibai ‘yan mata na garin Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a bara duk da cewa an kwato garuruwa da dama.

Babban Hafsan sojin kasar Janar Kenneth Minimah ya gayawa manema labarai cewa, rundunar sojin ta gudanar bincike a yankunan da aka kwato, amma duk da haka babu wanda ya ce ya san inda su ke.

A ranar 14 ga watan Aprilun bara, kungiyar ta Boko Haram ta yi garkuwa da ‘yan matan a garin Chibok, lamarin da ya harzuka kasashen duniya ya kuma janyo kakkausan suka akan gwamnatin Najeriya na gazawa da ta yi na ba da kariya ga daliban.

Janar Minimah ya kara da cewa, a yanzu haka kungiyar na rike ne kawai da kananan hukumomi uku a jahar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, baya ga cewa an fatattaki ‘yan kungiyar baki daya daga jihohin Yobe da Adamawa.

Babban Hafsan Sojin na Najeriya ya kuma ba da tabbacin cewa za su kwato sauran garuruwan Gwoza da Kalabaldi da kuma Abadam.

Yayin da aka tambayeshi shin ko za a gudanar da zabe a wadannan yankuna, sai ya ce, wannan batu ne da hukumar zabe ta INEC za ta amsa.

A ranar 28 ga watan nan na Maris ‘yan Najeriya za su kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa, bayan da aka dage gudanar da shi a watan Fabrairun da ya gabata saboda dalilan tsaro a arewa maso gabashin kasar.