Babu Batun Tsagaita Wuta a Syria

Yau Talata Majalisar Dinkin Duniya tace ta sami rahotannin dake cewa ana ci gaba da fada a yankin da ke karkashin ‘yan tawaye na gabashin Ghouta a Syria, wanda ya kamata ace yana karkashin yankunan da Rasha zata dakatar da kai farmaki domin baiwa fararen hula damar ficewa daga yankin.

A cewar maigana da yawun hukumar agaji ta MDD, Jens Laerke, “a bayyane yake abin da ke faruwa a yankin, ba zai baiwa tawagar agaji damar shiga ba, ko kuma ya bada damar kwashe mara sa lafiya ba ba.”

Rasha da Syria na zargin mayakan ‘yan tawaye da kai hare hare wadda ya shafi hanyar shiga yankin, suka c e farmakin ya kuma taba wasu yankuna a Damascus, zarginda ‘yan tawayen suka musanta hakan.

Kungiyar kare hakkin bil Adama dake sa ido a Syria mai suna “Observatory”,a tsawon shekaru bakwai na yakin, tace wani hari ta sama da ya afkawa gabashin Ghouta, yankin da ya fuskanci karin tarzoma a baya bayan nan har ya haddasa mutuwar daruruwan mutane. Sai dai dakarun Syria sun musanta kai harin.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya fada jiya Litinin cewa, Rasha zata tsagaita wuta daga karfe 9 na safe zuwa karfe 2 na rana a gogon Syria.