Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala Sheik Sani Yahaya Jingir, wanda ya saba ragargazar akidar ‘yan Boko Haram, yace kungiyar ta ‘yan Sunnah na murna da zaman lafiya da ya fara dawowa musammam ma a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Dattijon kungiyar Sa’idu Hassan Jingir, yayi kira ga jama’a da a so juna a kuma hada kai, da yafewa juna kura kurai, haka kuma yayi kira da ayiwa shugaban Najeriya addu’ar fatan al-khairi.
Shahararren malamin nan mai wa’azi Sheik Hamza Adamu Abdulhamid, yace kungiyar zata ci gaba da karantar da akidar gaskiya don yaki da gurbatattun akidu, da nuna illar barayin biro.
Kungiyar dai nayin irin wadannan wa’azi ne a Abuja duk shekara, da reshen kungiyar karkashin Sheik Ibrahim Duguri. Taron dai ya tashi da batun gidauniyar karasa cibiyar Islama da babban Masallaci da kungiyar ke ginawa a unguwar Gutsafe dake Abuja.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5