Batun yawan aukuwar gobara a kasuwannin Najeriya na cikin matsalolin dake haifar da koma baya ga cigaban 'yan kasuwa da hadahadar kasuwanci a kasar.
Ko a makon jiya gobara ta lalata kayayyaki na miliyoyin nera a kasuwar Singer dake Kano.
Wata tawagar majalisar wakilan Najeriya bayan ta yi rangadin wuraren da gobara ta lalata da kuma jajajantawa 'yan kasuwar da lamarin ya shafa ta gana da shugabannin cibiyar kasuwanci, masana'antu da ma'adanai da ayyukan noma ta jihar Kano Onarebul Alhassan Ado Doguwa shugaban tawagar ya yi karin bayani.
Yace a cikin shirin da suke dashi a kwamitance da kuma ikon da majalisa ta basu ya hada da tattaunawa da shugabannin al'umma da sarakunan gargajiya da shugabannin kwararru da zasu basu shawarwari da za'a iya kare yawaitar aukuwan gobara.
Daya daga cikin matakan da zasu dauki a kwamitance shi ne ba majalisar shawara ta yadda za'a iya yin dokokin kiyaye aukuwar haduran wuta. Ma fi yawan haduran wuta da ake samu a kasuwanni suna faruwa ne bayan an rufe kasuwanni da yawan dauke wuta da ake samu da yin anfani da wayoyi marsa inganci.
Tana yiwuwa majalisa ta kafa dokar hana shigowa da wayoyin wuta da basu da inganci da kuma haba harkokin tsaro ciki da wajen kasuwanni. Yin anfani da naurorin zamani don hana aukuwar gobara zasu taimaka.
Alhaji Dalhatu Abubakar mataimakin shugaban cibiyar kasuwanci yace suna da babban tsarin baiwa gwamnatin Najeriya shawara kan yadda yakamata ta tallafawa harkokin kasuwanci. Masana'antu da yawa sun durkushe domin babu wuta kana mutane suna nan babu aikin yi domin sun rasa jarinsu. Saboda haka dole ne sai gwamnati ta shigo ta taimakawa 'yan kasuwa.
Ga karin bayani.