Babban kamfanin mai na gwamnatin kasar Saudiyya a karshe dai ya bude kofa ga ‘yan kasuwa a jiya lahadi, inda ya bada sanarwa kan niyyarsa ta bude kofa ga masu saka jari na cikin gida na abinda ake ganin zai iya zama harkar sayar da hannun jari mafi girma a duniya, a cigaba da kokari da masarautar ta ke yi na karkatar da harkokin tattalin arzikinta daga dogaro ga mai.
To amma a wannan sanarwar ta shi, wadda aka jima ana jira, kamfanin Aramco, wanda shi ne kamfani da ya fi ko wanne samun riba a duniya, bayanai kadan kawai ya yi kan yawan adadin hannun jarin da za su sayar, da farashin da kuma ranar da za a kaddamar.
Shugabannin wasu bankuna sun fada wa gwamnatin Saudiyya cewa mai yiwuwa ‘yan kasuwa su kiyasta darajar kamfanin kan kudi dala tiriliyan daya da rabi, wato kasa da Tiriliyan 2 da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman ya dauka darajarsa ta kai a lokacin da ya fara kawo shawarar sayar da hannun jarin kamfanin kusan shekaru hudu da suka gabata.
Kamfanin na Aramco bai bayyana irin matakan da zai dauka na tsaro ba, biyo bayan wani mummunan hari da aka kai kan wasu matatun man sa a cikin watan Satumba.