Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Chile Ta Shammaci Amurka


Hukumomin kasar Chile, sun shammaci Fadar White ta Amurka, bayan da suka soke wasu tarukan koli biyu, ciki har da wanda shugaban Amurka Donald Trump zai halarta a watan gobe, inda za su gana da Shugaba Xi Jinping na China.

A jiya Laraba shugaban Chile Sebastine Pinera, ya fid da sanarwar, inda ya ce ba za su karbi bakuncin taron tattalin arziki na hadin kan kasashen yankunan Asiya da Pacific ba, wanda ake kira APEC a takaice, saboda zanga zangar masu adawa da gwamnati da ake yi a Santiago, babban birnin kasar.

Shugaba Pinera ya ce, “abu na farko da ke gabanmu a matsayinmu na gwamnati, shi ne mu maido da doka da oda, tsaron al’umar kasa da tabbatar da zaman lafiya.”

Shugaba Trump dai ya so ya yi amfani da taron, wajen rattaba hannu a sashi na farko kan matsayar cinikayya da suka cimma da China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG