Akwi alamar tambaya dangane da abun da ya faru a Cibok domin sabili da tsoron kada 'yan Boko Haram su kai hari akan makarantun gwamnatin jihar ta rufesu. Da zata kirawo yaran domin yin jarabawar kammala karatun sakandare, meyasa ba'a shirya masu ingantacen tsaro ba?
WASHINGTON, DC —
Bisa ga duka alamu gwamnatin jihar Borno bata shiryawa daliban makarantar Chibok ba wani ingantacen tsaro kafin tace su dawo su rubuta jarabawar kammala karatun sakandare.
Mrs. Hannatu Ibrahim daya daga cikin wakilan taron kasa mai wakiltar Gombe ta yi wasu tambayoyi da dama dangane da 'yan matan da 'yan bindiga suka sace a makarantarsu dake Chibok. Tace bayan an rufe makarantu sabili da barazanar 'yan kungiya Boko Haram menene dalilin sake kiran 'yan matan su koma makarantarsu ba tare da shirya masu tsaro ba? Da gwamnati tace su koma me yasa bata kawo jama'an tsaro ba domin su kare lafiyar yaran lokacin da suke rubuta jarabawa?
Kamata yayi gwamnati tayi shirin kare yaran yadda ba za'a kai masu hari ba ko a tafi da su kamar yadda ya faru. Yanzu da 'yan bindiga suka kwashesu babu wanda ya san abun da zai faru da su.
A arewa maso gabas ana fama da mace-macen mata lokacin haifuwa sai gashi wadanda zasu zama iyayen gobe sun fada cikin wani mawuyacin hali. An hana su samun ilimin da zasu yi anfani da shi su taimakawa kasarmu. Dole lamarin ya tada mana hankali ya kuma bata mana rai.
A arewa akwai iyaye sarakuna. Idan bako ya shigo gari ana sani amma yanzu yaya aka yi har wasu dari biyar ko da fi su shigo gari ba'a sani ba? A da kafin mutum ya shigo gar an san da shi. Mama Hannatu tace ran mata ya baci shi yasa duk matan dake cikin taron kasa suka sa bakaken kaya domin nuna bakin cikinsu.
Idan ba'a yi hatara ba abun dake faruwa a arewa maso gabas zai yadu a kasar. Idan hakan ya faru an kashe kowa da kowa to wa gwamnonin ko shugaban kasa zasu yi mulki a kansu?
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5