Shugaba Issuhu ya bayyana hakan ne yayin da ake bukuwan cika kasar ta Nijar shekaru 58 da zama jamhuriyya.
A 'yan kwanakin baya, rahotonni sun yi ta yawo cewa shugaban na da niyyar yin tazarce idan ya kammala wannan wa'adin na sa na biyu.
Amma Issuhu ya ce burinsa shi ne ya mika mulki ga zababbiyar gwamnatin da jama'a su ka zaba.
Shugaban ya kara jaddada anniyarsa ta ci gaba da yin yaki a fannoni daban daban na kasar.
Daga akwai fannin yaki da cin hanci da rashawa da kwararar bakin haure da kuma murkushe ayyukan ta’addanci.
Kana shugaban ya sha alwashin ci gaba da tabbatar da an kawar da matsalar masu toye hanyoyin biyan kudaden haraji.
To sai dai tuni wasu ‘yan kasar su ka fara tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke yabawa, wasu kuwa suka su ke yi musamman daga bangaren ‘yan adawa.
Jamhuriyar ta Nijar na bukuwan sallar samun ‘yancin kai ne a karo na 58, bayan da turawan mulkin mallaka na Faransa su ka raine su.
Domin jin ra’ayoyi mabanbanta dangane da wannan lamari saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5