Ba Zan Yi Ritaya Ba Bayan Gasar Cin Kofin Duniya - Ronaldo

Cristiano Ronaldo

Dan shekara 37, Ronaldo, wanda dan asalin kasar Portugal ne, ya ce yana da burin ya ga ya taka leda a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a 2024, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo, ya ce ba zai yi ritaya ba bayan an kammala gasar cin kofin duniya a wannan shekara.

A watan Nuwamba za a fara gasar, wacce kasar Qatar za ta karbi bakunci.

Dan shekara 37, Ronaldo, wanda dan asalin kasar Portugal ne, ya ce yana da burin ya ga ya taka leda a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a 2024, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Ronaldo ya bayyana hakan ne a wani taro da aka yi a ranar Talata bayan da hukumar kwallon kafar kasarsa ta Portugal ta karrama shi, saboda zarra da ya yi wajen zura kwallaye.

Tun a farkon shekarar nan Ronaldo ya yi watsi da raderadin da ake yi, na cewa zai yi ritaya bayan an kammala gasar cin kofin duniya a Qatar.

Dan wasan dai na ta fuskantar tarnaki a kungiyarsa ta United inda ba kasafai ake saka shi a farkon wasa ba.