Ba Zan Yi Murabus Ba – Secondus

Uche Secondus (Facebook/ PDP)

“‘Yan tsirarun mutanen da ke son ya yi murabus su fito karara su fadawa mambobin jam’iyyar da ke duka fadin kasar, laifin da ya yi da suke so ya yi murabus.”

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus ya ce babu abin da zai yi ya ajiye aikinsa saboda a cewar shi, bai ga laifin da ya yi ba.

Secondus na fuskantar kiraye-kirayen ya yi murabusa daga mukaminsa.

Gwamnonin jam’iyyar ta PDP na gudanar da wani taro a ranar Litinin a Abuja don bayyana matsayarsu kan wannan takaddama.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP a Najeriya, Gwamna Sokoto Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ne yake shugabantar zaman.

Sai dai Secondus, wanda ya yi magana ta bakin mai taimaka masa a fannin yada labarai Ike Abonyi kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito, ya ce babu abin da zai sa ya yi murabus.

Masu neman ya yi murabus daga mukaminsa, na zargin cewa Secondus ne da alhakin sauya sheka da wasu gwamnonin jam’iyyar suka yi, saboda abin da suka kira rashin iya shugabancinsa.

Baya ga gwamnonin da suka koma APC, a kwanan nan wasu kushoshin jam’iyyar da ke kwamitin gudanarwa sun ajiye aikinsu, a wani mataki na nuna borensu kan yadda Secondus yake tafiyar da jam’iyyar.

Amma shugaban jam’iyyar, ya ce “‘yan tsirarun mutanen da ke son ya yi murabus su fito karara su fadawa mambobin jam’iyyar da ke duka fadin kasar, laifin da ya yi, da suke so ya yi murabus.”

Rahotanni daga Abuja na cewa wasu matasa sun yi zanga-zangar goyon bayan neman Secondus ya yi murabus a kofar ofishin hedkwatar jam’iyyar.