Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Nemi ‘Yan Najeriya Su Taya Ta "Ceto Kasar Daga Hannun APC"


Atiku Abubakar, hagu tare da gwamna Wike, hagu (Facebook/PDP)
Atiku Abubakar, hagu tare da gwamna Wike, hagu (Facebook/PDP)

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce miliyoyin ‘yan Najeriya sun zaku su yi rijista da jam’iyyar yayin da take shirin fara aikin sabunta rijista ta yanar gizo a duk fadin kasar.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo gabanin fara aikin rijistar a ranar Litinin cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaranta Kola Ologbondiyan.

"Jam’iyyar PDP ta ga tururuwar miliyoyin ‘yan Najeriya da suka nuna cewa sun kimtsa don yin rijistar, wanda za a yi a duk fadin kasar, tun ma gabanin a fara, kamar yadda aka tsara a ranar za a yi Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.”

Jam’iayyar ta lura da haka, “bisa yadda miliyoyin ‘yan Najeriya a dukkan shiyoyin kasar shida suka yi ta kira don neman karin haske kan yadda za su yi rijistar, sa’a 24 kacal bayan da aka fid da sanarawar aikin rijistar.

Sanarwar ta Ologbondiyan ta kara da cewa, “wannan sha’awa da dumbin ‘yan Najeriya suka nuna don yin rijista da jam’iyyar, wata alama ce da ke nuna cewa za su goyi bayanmu wajen ceto kasarmu daga shugabancin APC.”

A dai watan Afrilun bana, jam’iyya mai mulki ta APC ta gudanar da nata aikin sabunta rijistar mambobinta.

A ranar Alhamis tsohon mataimakin shugban Najeriya Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa ‘yan Najeriya sun zaku PDP ta karbi mulki a matakin tarayya a 2023.

Atiku, wanda ya kara da shugaba Muhammadu Buhari a 2019, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan ganawar da ya yi da gwamnan jihar Rivers Nyesom Ezenwo Wike a Fatakwal.

Atiku, wanda ya kara da shugaba Muhammadu Buhari a 2019, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan ganawar da ya yi da gwamnan jihar Rivers Nyesom Ezenwo Wike a Fatakwal.

Ita dai jam'iyya mai mulki ta sha fadin cewa PDP ce musabbabin halin kuncin rayuwa da 'yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki, tana mai cewa ayyukan da take yi, gyara ne kan barnar da PDP ta yi cikin shekara 16 da ta yi tana mulki.

XS
SM
MD
LG