Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana cewa yana matukar ganin mutuncin Shugaba Bola Tinubu da ba zai iya sukarsa ba.
An sha jiyo muryar sanatan a kan batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arziki karkashin mulkin Tinubu.
Sanatan wanda ya bayyana a shirin siyasar tashar talabijin ta Channels na jiya Talata ya musanta zargin cewa yana adawa da Shugaba Tinubu sai dai yana sukar manufofin gwamnatinsa ne kawai.
“Ba shugaban kasar na ke suka ba illa manufofinsa. Ni ba mai adawa da gwamnatin nan ba ne, ai gwamnatinmu ce.”
“Ba na sukar na gaba dani, mahaifina soja ne kuma a bariki muna mutunta na gaba damu.
"Tinubu na gaba da ni ne kuma ina mutunta shi sai dai na saba da shi a wasu bangarorin da na ke fatan za mu daidaita,” a cewar Ndume.
Da yake sharhi kan yadda Najeriya za ta shawo kan manyan matsalolin dake damunta, Ndume ya bukaci Shugaba Tinubu da ya mayar da hankali kan aiwatar da kasafin kudin gwamnatin tarayya tare da bada fifiko a kan muhimman bangarori irinsu tsaro da walwalar al’umma.