Wannan ya biyo bayan rashin zuwan wasu shugabani hukumomi ne a lokacin zaman kare kasafin kudin shekara 2024, kamar yadda doka ta tanada.
Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Dattawa Solomon Adeola Olamilekan ya koka kan yadda wasu shugabannin hukumomin Gwamnati ke kin bayyana a gaban kwamiti domin kare kasafin kudin ma'aikatun su.
Olamilekan ya ce batun rabon kudi domin yi wa jama'a aiki muhimmin lamari ne a tsarin dimokaradiyya, saboda haka yana kira ga shugaban kamfanin mai na NNPC da ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Alhamis.
Ya kuma kara da cewa akwai wasu batutuwa na kudi har Naira tiriliyan 11 da Mele Kolo Kyari zai yi bayani a kan su.
A lokacin da ya ke jawabi kan muhimmancin sauraron bahasi da bayanan masu ruwa da tsaki kan kasafin kudin, Sanata mai wakiltan jihar Naija ta Gabas kuma shugaban kwamiti kudi Mohammed Sani Musa ya ce taro ya yi kyau, domin tattaunawa kan kasafin kudi zai ba da damar majalisa ta himmatu wajen tsara shi daki-daki.
Sani ya ce Majalisa za ta sa ido a wani sabon tsari na kawar da cushe da aringizo a kasafin kudin, inda za’a samar da wata na'ura da za ta taimaka wajen yin wannan gagarumin aiki.
Da yake yin tsokacin kan kasafin kudin, shugaban jam’iyyar SDP ta kasa, Shehu Musa Gabam, ya ce akwai abin dubawa a wannan kasafin kudin.
Gabam ya ce wannan kasafi ne da aka yi domin masu hali, ba domin talakan kasar ba, saboda haka suna ba Majalisa shawara ta gyara kasafin domin ya yiwa 'yan kasa amfani.
A bangaren Majalisar Wakilai kuma, Kwamiti ne ya ba da umurnin a kamo Gwamnan Babban Bankin Najeriya Olayemi Cardoso da Akanta Janar na Kasa Madan Oluwatoyin Madein da wasu manyan mutane 17.
Kwamitin ya nuna rashin gamsuwarsu da kin halartar zaman sauraren bahasi da suka yi.
Sauri cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5