Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Samu Ƙarin Kuɗin Shiga Zuwa Tiriliyan Ɗaya Cikin Wata Huɗu


Olawale Edun
Olawale Edun

Ministan kuɗin Najeriya ya bayyana cewa Najeriya ta samu ƙarin kuɗin shiga cikin wata huɗu bayan sauye-sauye da kuma cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu yayi, sai dai 'yan Najeriya na ganin ƙarin kuɗin shigar ba wani tasiri zai yi a ƙasar ba, idan har talakawan ƙasar basu gani a ƙasa ba.

Ministan kuɗi da kuma bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, Olawale Edun, ya bayyana hakan ne a lokacin buɗe taron bita a kan rarraba kuɗaɗen shigar ƙasar a Jihar Delta.

Edun, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ayyuka na musamman na ma’aikatar kuɗi ta tarayya, Mista Okokon Ekanem, ya ce a cikin watanni shida na gwamnatin Bola Tinubu, al’ummar ƙasar sun shaida wasu muhimman sauye-sauye da suka haɗa da batun cire tallafin man fetur, gyaran fuska ga kasafin kuɗi da na hada-hadar kuɗi da nufin gyara manufofin inganta shigar kuɗin ƙasar.

Edun, ya ƙara da cewa daidaito da sauƙaƙe gudanarwar haraji tare da cimma kasuwar canjin kudi ta bai ɗaya, sun taimaka wajen samun kuɗin shiga."

Ministan ya ƙara da cewa sanin kowa ne tallafin man fetur abu ne da bashi da tabbas, kuma yana daga cikin abin da ke taɓarɓarar da tattalin arzikin ƙasar, a don haka aka cire tallafin domin a inganta rayuwar al'ummar Najeriya.

Edun ya kuma ce cikin watanni huɗu kacal, kuɗin shigar ƙasar ya ƙaru daga naira Biliyan 650 zuwa Tiriliyan 1.

A hirarsa da Muryar Amurka, Nasiru Shu'aibu Marmara, masani kuma manazarci kan lamuran da suka shafi tattalin arziki da ci gaban ƙasa, ya ce wannan labari ne mai daɗin ji, kuma kamata yayi samun ƙarin kuɗin shigar ya taimaka wa ƙasar wajen rage cin bashin da take yi, kazalika talakawa su gani a ƙasa ta bangaren inganta rayuwarsu ta yadda zasu samu sauƙin abubuwa.

'Ƴan ƙasar dai sun bayyana rashin tabbas dangane da tasirin ƙarin kuɗin shigar da ƙasar ta samu, inda suka ce irin wannan labarin ba sabon abu bane a wajensu kuma basa gani a ƙasa.

'Ƴan Najeriya dai na fatan ganin sauyi mai amfani garesu, domin kawar musu da shakkun gafara Sa, basu ga ƙafo ba.

Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG