Dan majalisar ya ce ko shakka babu akwai wasu garuruwan da aka kwato amma idan aka yi la'akkari da yadda garuruwan suke yanzu akwai bukatar jirkintawa.
"Jirkintawar za ta taimaka a samu a sake gina masu muhallansu. Yakamata a tanada masu ruwan sha da harkokin kiwon lafiya da kuma wasu bukatu na yau da kullum." In ji Muhammad Maina.
Banda samarda ruwan sha yace garuruwan suna wari kuma zama cikinsu yanzu zai yi wuya. Ya ce za'a kwashe kusan shekara biyu ana gine-gine da wasu ayyukan kafin mutane su iya komawa. A cewar dan majalisar garuruwan basa zaunuwa yanzu.
Shi ko shugaban karamar hukumar Galaho, Abdulrahaman Abdulkarim ya ce duk da cewa da hadin gwiwar sojojin Chadi an kwato garinsu amma bayan da sojojin suka koma kasarsu 'yan Boko Haram sun sake afkawa garin inda suka hallaka wasu mutanensu..
Alhaji Khalifa Bukar Ram shugaban karamar hukumar Kalebage ya ce har yanzu garinsu na hannun 'yan Boko Haram. Ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta yi wani abu akai.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5